Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa za ta maido wa Najeriya akalla kudade kwatankwacin dala milyan 321 daga dimbin dukiyar kasar nan da tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya sace.
Maido da wannnan kudin dai ya biyo bayan wata yarjejeniya ce da aka kulla tsakanin kasar Switzerland, Najeriya da kuma Bankin Duniya.
Idan za a iya tunawa, kungiyar rajin yaki da cin hanci da rashawa, Transparency International, ta zargi Abacha da satar makudan kudaden kasar nan da ta ce sun kai dala bilyan 5 a cikin shekaru biyar, tsakanin 1993 zuwa lokacin rasuwar sa, 1998.
Cikin 2014 ne dai Najeriya da iyalin Abacha suka cimma yarjejeniyar za a maido kudaden Najeriya.
Najeriya ta yi haka ne a bisa sharadin cewa idan aka dawo da kudin to za ta janye tuhumar da ake yi wa daya daga cikin’ya’yan Abacha, mai suna Abbba Abacha.
Kasar Switzerland dai ta caji Abba da laifin wawurar kudade daga Najeriya aka damfare su a kasar. An kuma caji Abba da laifin fojare cikin Afrilu, 2005, bayan Jamus ta koro shi daga kasar. Abba ya shafe kwanaki 561 a tsare.
Cikin 2006 ne kasar Luxermburg ta bada odar cewa ta kwace duk wasu kudade da Abacha ya tara a kasar.
To amma ita gwamnatin Switzerland, ta yi yarjejeniya tare da hadin kai da bankin duniya cewa za ta maido wa Najeriya kudin, amma ba za ta damka kudin a hannun Najeriya ba.
Za a damka kudin ne ga Bankin Duniya, inda shi kuma zai rika amfani da kudin ya na gudanar da ayyukan raya kasar da Nijeriya za ta rika yi da kudaden.
Za a rika gudanar da ayyukan rasa kasa da kyautata rayuwar marasa karfi da galihu ne a yankunan karkara.
Discussion about this post