Gwamnati za ta samar wa fannin kiwon lafiya isassun kudi – Buhari

0

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ware isassun kudade domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a ziyar da kungiyar likitoci MDCAN ta ziyar ce shi a fadar shugaban kasa ranar Asabar da ya gabata.

Buhari ya kara da cewa inganta fannin kiwon lafiyar ‘yan Najeriya ne zai hana yawan fita neman lafiya a kasashen waje da mafi yawan ‘yan Najeriya ke yi.

Yayin da yake tofa albarkacin bakin sa kan bunkasa fannin kiwon lafiya shugaban kungiyar MDCAN Ngim Ngim ya yi kira ga gwamnati da ta karawa shugabanin mayan asibitocin kasar nan yawan na aiki kafin ayi musu murabus.

Bayan haka kuma yayi kira ga gwamanti ta gina jami’o’in koyar da aikin likitanci a kasar nan sannan ta tsara hanyoyin kawar da rashin jituwar dake tsakanin ma’aikatan fannin kiwon lafiya dabam dabam na kasar nan.

Share.

game da Author