Gwamnati za ta gina tashoshin wutan lantarki a Abuja, Kaduna da Kano

0

Kamfanin mai na kasa NNPC na shirin gina wasu tashoshin samar da wutan lantarki da zai samar da wuta kimanin kilowatt 4,600 a jihohin Kaduna, Kano da babban birnin tarayya Abuja.

Ministan Albarkatun mai Ibe Kachikwu ya ce tashoshin za su yi aiki ne da iskar gas wanda za a samar da su ta bututtun iskar gas da ya taso daga Ajakuta zuwa wadannan tashoshi.

” Za a karo iskar gas ta bututun da ya taso daga Warri da kuma sauran wuraren da ake sarrafa iskar gas din dake ke kudanci kasar nan.”

Kachikwu ya fadi haka ne da ya ke gabatar da takardun kwangilar wannan aiki domin amincewa kwamintin zartaswa.

Bayan haka shugaban NNPC Maikanti Barau ya bayyana wa gwamnan jihar Neja Abubakar Bello cewa gwamnati zata ci gaba da neman mai da take yi a garin Bida.

Share.

game da Author