Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya nada kanwar sa Ogechi Ololo sabuwar kwamishinar samar da farin ciki ga mutane a jihar da kara musu karfin guiwar samun nasara ga duk abin da suka sa a gaba.
Sanar da nada Ololo ke da wuya sai mutane suka fara caccakar gwamnan kan nada kanwar sa kwamishinan farin ciki.
Da yawa daga cikin mutanen jihar da suka tofa albarkacin bakin su akai sun yi Alla wadaran wannan nadi da akayi, scewa basu wani amfani da zai yi wa jihar ba.