GANGAMIN PDP: An Gyara ne, Ko An Sake Dagulawa

0

Gangamin jam’iyyar PDP dai ya wuce, inda masu jefa kuri’a 2114, suka taru suka zabi sabbin shugabanin jam’iyyar na kasa baki daya.

Uche Secondus ne ya zama shugaba daga cikin ‘yan takara 72 da suka nemi mukamai daban-daban har 21.

Tun kimanin makonni biyu kafin Gangamin Jam’iyyar PDP wanda aka yi jiya Asabar a Abuja, alamomi da dama sun nuna cewa ba ita ce jam’iyya mai mulki ba, kuma jam’iyyar na jin jiki sosai.

Akwai dai rashin mulki a hannu, akwai kuma rashin kudi a cikin babban aljihun jam’iyyar, sannan kuma da yawan wadanda suka ci moriyar ta daga cikin manyan ta, an daina jin motsin su – sai dai motsin masu neman takara kawai.(Premium Times Hausa)

RASHIN KUDI:

A shekarun baya, idan PDP za ta yi taron Gangami a Abuja ko ma a ina ne, an rika cika jaridun kasar nan da tallace-tallacen ‘yan takara. A gefe daya kuma a rika kururuta jam’iyyar da talloli a gidajen radiyo na ‘yan takara da kuma kalamai ha cika wa sauran jam’iyyu idanu, kamar yadda jam’iyyar ta rika kiran manta “jam’iyyar da ta fi karfi a Afrika” ko kuma “sai PDP ta yi mulki shekara 60 sannan za ta hakura wata jam’iyya ta kama.”

Sai ga shi a jawabin Shugaban Riko na Jam’iyyar, Ahmed Makarfi a wurin taron jiya, ya bayyana cewa naira milyan 2 ce kacal ta rage a cikin asusun ajiyar PDP.
(Premium Times Hausa)

Akwai wani rahoto da ya nuna kungiyar direbobin manyan motoci ta kasar nan, ta na da kudi a asusun ta, sama da naira milyan 100.

MAHALARTA GANGAMIN PDP:

A lokacin da PDP ke mulki, idan jam’iyyar na gudanar da gangami a Abuja, birnin da garuruwan da ke kewaye da shi kan yi cikar-kwari da ‘yan Jam’iyyar daga ko’ina cikin kasar nan.

Sai dai abin ba haka ya ke ba, idan aka lura da yanayin yawan wadanda suka halarci taron gangamin jiya Asabar.

A lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya isa ya zauna a wurin gangamin, kusan babu kowa a bayan sa daga cikin manyan baki.(Premium Times Hausa)

Sabanin a zabukan baya, India akan cika wurin taron tun da sanyin safiya.

OTAL-OTAL

Maimakon a ce otal-otal din Abuja sun cika da manyan baki kamar yadda aka saba gani a gangamin PDP na shekarun baya, a wannan lokacin dai yawancin otal din Abuja ba su cika ba, wasu ma babu bakin da suka sauka ko da daya daga cikin su.

“A taron jam’iyyar a 2007, sai da muka je otal sama da 20 mu na neman inda za mu saukar da wani bako, amma ba mu samu daki ba.”
Haka Murtala Abdullahi wani ma’aikacin gidan wata jarida ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA.

Binciken da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar a jajibirin taron da kuma jiya Asabar ranar taron, otal da dama ba a cike su ke ba, kuma har ma neman bakin da za su saukar su ke yi ido rufe, ta hanyar rage kashi 20 ko 10 cikin 100 daga kudin kowane daki.

Avery Hotel da Progandi da sauran otal da ke Garki, Area 11 da Wuse Zone 2, duk ba su cika da masu taron gangamin PDP ba, kuma su na neman bakin da za su zauna a dakunan da ba kowa.(Premium Times Hausa)

A Progandy da ke Garki 2, mai bayar da daki ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa har dakunan Naira 7000 akwai, amma babu mai karba, saboda bakin ba su cika Abuja kamar shekarun baya ba.

KORAFE-KORAFE:

Kusan gaba dayan gangamin korafe-korafe ne ya lalata shi ko ya rage masa armashi. A bangaren wakilan Area masu Yamma, tun a jajibirin gangami aka samu rashin-jituwa a gidan Aminu Wali da ke Abuja.

‘Yan takara sun bijire sun ki yadda su janye wa wadanda aka nemi su janye. Wannan sabani ya yi kamarin da har sai da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya fusata ya fice daga wurin taron.

Daga bangaren manyan ‘yan takara kuwa, wadanda suka yi zargin an musu ba daidai ba, sun kasa daurewa, sun fito fili a akwatunan talbijin su na kwance wa PDP zani a kasuwa.

Dan takarar shugaban jam’iyya kamar Remond Dokpesi, Tunde Adeniran da Bode George, sun yi tir da zaben tare da muzanta ita kan ta jam’iyyar PDP, har su na yin ikirarin cewa a 2019, Buhari ya ci zabe ya gama, ko da bai yi kamfen ba, domin PDP ba ta dauko hanyar shirya kokawar kwace mulki ba.

SAMUN BARAKA A PDP:

Zaben ya fito da sabuwar baraka a jam’iyyar a fili. Na farko dukkan ‘yan takarar da su ka ki janyewa daga Arewa maso yamma, ba su samu nasarar lashe ko da mukami daya ba. Sannan kuma an haifar da babbar baraka tsakanin Kudu masu Yamma da kuma Kudu maso Kudu.

Wannan sabani zai iya gurgunta jam’iyyar ko kuma ya sa wasu su fusata su rika yi wa PDP zagon-kasa (anti-party).

SAKACIN PDP A GANGAMIN:

An ta yin tunanin cewa PDP za ta dauki wannan gangami da muhimmanci, ta hanyar zaburar da ‘yan Nijeriya zuwa ga matsalolin APC domin su guji jam’iyya mai mulki din.

Misali, ana ganin a lokacin APC ne matsalar garkuwa da mutane ta fi ta’azzara musamman a Arewa inda a kullum sai an sace mutane a jihar Kaduna an yi garkuwa da su.

Sannan kuma an fara gangamin a lokacin da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato, Damishi Sango, ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane su na neman a biya su naira miliyan 50, kafin su sake shi.(Premium Times Hausa)

A tunanin wasu, PDP za ta yi amfani da wannan da kuma yawan fadace-fadacen da ake yi a yankin Middle Belt tsakanin Fulani da manoma a matsayin makaman hujjojin ragargazar APC.

A maimakon haka, sai aka buge wajen rikicin shugabancin jam’iyya, wadda ba ta da komai a asusun ajiyar ta.

Ko ya za ta kasance idan an zo zaben fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban kasa da kuma na gwamnoni da sanatoci?

Ko jam’iyyar za ta sake saisaita kan ta kafin zaben dan takarar shugaban kasar da zai wakilci PDP? Shin bulkarar da aka yi a wurin zaben shugabancin PDP jiya a Abuja ba za ta sage guyawun masu neman canja sheka daga APC zuwa PDP ba?

Share.

game da Author