Yau Lahadi 24 Ga Disamba da kuma Talata 26 Ga Disamba ne Fadar Shugaban Kasa za ta rika yayata wani faifan bidiyo na Shugaba Muhammadu Buhari.
Bidiyon anyi shi ne da Turanci, kuma mai minti 55. Za a rika nunawa da bayyana kyawawan halayen Buhari, a matsayin mutumin kirki, mai tausayi kuma wanda ya damu da al’ummar sa.
Kakakin Yada Labaran Shugaba Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka jiya Asabar a Fadar Shugaban Kasa.
Faifan bidiyon dai zai kunshi wasu bayanai da kuma hirarraki da aka tattata wadanda aka yi da wasu hadiman shugaban kasa, masu yi masa ‘magori-wasa-kanka-da-kanka.
Za a rika nuno su su na bayyana halaye nagari na shugaban kasa da kuma irin tausayin sa ga ‘yan Najeriya. Ana zaton har irin barkwancin nan da raha da ya kan yi duk za a nuno.
Adesina ya ce za a gani kuma a nan wadansu halaye na Shugaban wadanda ba a sani ba.
To sai dai kuma tun bayan yin wannan sanarwa ne dimbim ‘yan Najeriya ke yin Allah-wadai da wannan bidiyo da za a nuna.
Da yawa na cewa bidiyon bai kamata ma a nuna shi a daidai wannan lokacin da ake tsananin wahalar mai ba. Sun kuma koka da yadda Fadar Shugaban Kasa ta kau da kai ga matsalar da ‘yan Najeriya Ke ciki ta bala’in tsadar fetur, suka karkata wajen tallata hajar su, wato Shugaba wanda hakan ya nuna ba gaskiya ba ne da su ke cewa Shugaba Buhari shugaba ne mai tausayi.
Masu adawa da wannan bidiyo wanda za a fara nunawa yau Lahadi da 8 – 9 na dare a Gidan Talabijin na NTA, sun ci gaba da karyata abin da bidiyon ya kunsa tun ma kafin a kalle shi.
Sun rika buga misali da yadda Buhari ke yin likimo, ya yi kunnen-uwar-shegu da wasu manyan matsalolin da ya kamata a ce ya gaggauta yin magana a kan su, amma sai ya yi kunnen-uwar-shegu, tamkar bai ma san da matsalar ba.
Idan za a iya tunawa, cikin watan Mayu, 2014, Buhari ya taba cewa, “rashin iya mulki ne a bar mutum ya shafe sa’o’i da yawa a layin mai. Wanda hakan zai shafi ci gaban kasa, domin an saki aiki an shiga layin mai.”
A yanzu da Buhari ke kan mulki, ‘yan bunburutu na sai da fetur har N400 kowace lita, amma ya kasa cewa komai. Kuma a daidai wannan lokacin ne za a tallata halayen sa na tausayin jama’a.