Erdogan ya gargadi kasashen Afrika da su guji bibiyan makarantu Turkish dake kasashen su

0

Farkon makon nan ne Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da sauran kasashen Afrika, su gaggauta cire ‘ya’yan su daga makarantun nan mallakar Turkish Schools, ya na mai cewa makarantun mallakar ‘yan ta’addar Turkiyya ne.

A wata hira da ya Yi da AllAfrica.com, kwanaki kadan kafin ziyarar da zai Kai wasu kasashe uku na Afrika, Sudan, Chadi da Tunisia, ya ce wata kungiya ce ke da makarantun, wacce ke fakewa da inganta ilmi ta na yada manufofi da aikata ta’addanci.

Ana la’akanta makarantun da kungiyar babban malamin nan da ke zaune a Amurka, mai suna Fethullah Gulen.

Gulen dai a da na hannun damar Erdogan nan, daga baya ya koma cikakken mai adawa dashi da gwamnatinnsa. Shi ne kuma ake zargi da yunkurin kifar da Gwamnatin Erdogan cikin watan Yuli, 2016, inda sama da mutane 250 su ka mutu.

“Mun gano wasu daga cikin su da hannu dumu-dumu, kuma an cafke su an yanke musu hukuncin dauri a kurkuku.

” Wadannan mabiyan Fethullah din sun zo da niyyar kashe ni da ni da dukkan iyali na, amma Allah ya kare ni daga sharrin su, da hare-haren bama-baman da su ka kai fada ta. Sai dai sun kashe masu tsaro na biyu. Gaba daya sun kashe mutane 29 a fadar tawa da su ka yi yunkurin kashe ni a wancan lokacin.’

“Don haka mu na gargadin dukkan ‘yan’uwan mu a Afrika su daina barin wadannan ‘yan ta’adda na rudar su da dimbin dukiya su na kafa makarantun fakewa su na yada ta’addanci.

“Cikin 1999 shugaban su Fathullah ya tafka laifi, ya tsere Amurka, kuma tuni mu ka nemi Amurka ta dawo mana da shi a Turkiyya domin mu hukunta shi.”

Daga nan sai Erdogan ya yi barazanar cewa muddun Amurka ba ta maida Gulen Fathullah zuwa Turkiyya ba, domin ya fuskanci tuhumar ta’addanci ba to ba za su taba yarda da bukatun Amurka na a tura mata gudaddun ‘yan ta’addar da ke tsare a Turkiyya domin su fuskanci tuhuma a Amurka.

“Mun cika manyan akwatai har 84, makare da tulin hujjojin da ke nuni da cewa Gulen Fathullah mai makarantun Turkish Collage shi ne gogarman ‘yan ta’addar da su ka nemi kifar da gwamnati na, ta hanyar kokarin kashe ni da kuma share iyali na kaf a doron kasa.

“Amma a gobe idan Amurka ta nemi na tura mata wani ko wasu ‘yan ta’adda domin ta hukunta su, zan ce ba zan tura mata ba, domin ita ma ta bai wa Gulen babban dan ta’addar da ya jagoranci kashe mutane 252 a Turkiyya mafaka a Amurka.

Daga nan sai ya ce kasar Turkiyya ta fito da wasu tsare-tsaren ilimi wanda za su maye gurbin makarantu masu alaka da Gulen, kuma tuni an fara aiki da su a kasashen da zai kai wa ziyara.

Sai dai kuma yawancin kasashe ba su yi na’am da bukatar Erdogan ba, ciki kuwa har da Najeriya.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Enyeama, ya tabbatar da samun wasikar Shugaba Erdogan na Turkiyya. Sai dai kuma ya ce ‘yan Turkiyya mazauna Nijeriya, walau masu gudun hijira ko masu zama don kan su, su da kariya a karkashin jarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya cewa ba za a maida su kasar Turkiyya ba.

Ita ma Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an samu canji dangane da yadda ake tafiyar da makarantun Turkish Collages a kasar nan, ta hanyar shigar da ‘yan kasa a cikin shugabannin makarantun.

Share.

game da Author