Gwamnan jihar Kaduna NAsir El Rufai ya nuna bakincikin sa ga harin da wani dan bindiga ya kai kauyen Nindem, dake Godogodo, karamar hukumar Jema’a jihar Kaduna.
Wani dan bindiga ya bude wa cincirindon wasu mazauna kauyen Nindem, dake Godogodo karamar hukumar Jema’a, Jihar Kaduna wuta.
Kamar yadda rahotannin suka iske mu, mutumin dai ya shigo wannan kauyen shi kadai ne dauke da bindiga a daidai mutanen kauyen na gudanar da shirye-shiryen bukin Kirismeti da za ayi ranar Litini mai zuwa sannan ya bude wuta.
Mutane hudu ne suka rasa rayukansu a harin inda wasu da dama suka sami raunuka.
Shugaban rundunar tsaro na Operation safe haven ya ce tuni rundunar sa ta kama wadansu amma ana bincike akai.
Yace zaman Lafiya ya dawo kauyen.
El-Rufai ya roki mutanen yankin da su zauna lafiya da juna, yana mai cewa jami’an tsaro ba za suyi kasa-kasa ba wajen ganin sun taso keyar duk wanda yake da hannu a aikata wannan mummunar aiki.
Samuel Aruwan ne ya sanya hannu a takardar.
Discussion about this post