EFCC ba ta da ikon kama alkalan da ke kan aikin su – Kotun Daukaka Kara

0

Kotun Daukaka Kara ta Lagos, ta yanke hukuncin cewa Hukumar EFCC ba ta da karfi, iko ko iznin kama duk wani alkalin da ke kan aikin sa, har sai idan wannan alkalin Hukumar Kula Da Alkalai ta Kasa ce ta kore shi daga aiki, sannan za a iya cafke shi.

Alkalin Kotun Daukaka Kara da ke Lagos, Hydiazira Nganjiwa ne ya yanke wannan hukunci a yau Litinin a Lagos.

Akwai alkalai masu tarin yawa da wadanda EFCC ta gurfanar a kotuna daban-daban, wadanda ke fuskantar tuhumar cin hanci, cuwa-cuwa da kuma baddala shari’au, cikin su kuwa har da Alkaln Kotun Kolin Najeriya.

Share.

game da Author