Gwamnatin tarayya ta sanar da bude wani shafi domin masu bukatar yin aiki da gwamnatin tarayya.
Akwai wuraren aiki masu dama a wasu ma’aikatun gwamnati wanda ake bukatar a cika su.
Anyi kira ga masu bukata da su je shafin www.fedcivilservice.gov.ng a yanar gizo domin cika fom din.
Bayan haka za a iya karbar fom din neman aikin domin cikawa a jihohi.