Dalilin da ya sa likitocin Najeriya ke waske wa kasashen waje don neman aikin yi

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA Mike Ogirima ya ce a shekarar 2016 likitoci 300 ne suka fice daga kasar nan zuwa kasashen wajen don neman aiki.

Ya fadi haka ne bayan taron kwamitin zantaswa da aka yi ranar Alhamis.

Ya kuma ce ya ji labarin cewa wasu likitoci 500 sun rubuta jarabawar samun kwarewar aiki domin samun aikin a kasashen waje.

” A yanzu haka cikin likitoci 72,000 da suka yi rajista da kungiyar mu 35,000 na aiki a kasashen waje kamar su Amurka da Landan.”

Ogirima ya ce kasar nan za ta iya magance wannan matsalar ta hanyar amince wa da kudirin nan da zai inganta fannin kiwon lafiya da ma’aikatan ta.

Daga karshe Abimbo Olajide na kungiyar likitoci na kasa NARD ta ce a ra’ayin ta Najeriya na horar wa kasashen waje ne likitoci ba wai don su gama su yi aiki a nan na.

Share.

game da Author