Sanata Ben-Murray Bruce ya koka kan yadda akayi watsi da inganta fannin shakatawa a kasar nan.
Sanata Bruce ya fadi haka ne a shafin sa na Twitter da yake yin tsokaci kan watsi da harkar da akayi a kasar nan.
Ya ce akwai wani fim da aka shirya shi a kasar Amurka mai suna ‘Star Wars’ Wanda ya kawa kudin shiga sama da kasafin kudin Najeriya na Shekarar 2018.
“Idan kasar nan ta mai da hankali wajen inganta wannan fannin sai ya fi mai samar mata da kudaden Shiga.”