Da kudin sata aka kafa gwamnatin Buhari, Batun yaki da rashawa da ya ke yi, duk burga ce kawai, cewar Baba-Ahmed

3

Wai jigo a jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar ya na mai cewa sam Buhari bai iya mulki ba, kuma shi ma tsamo-tsamo ya ke cikin daka-daka.

Yusuf Datti Baba-Ahmed, wanda jigo ne a APC ta jihar Kaduna, kuma ya taba yin dan majalisar tarayya a tsakanin 2003 zuwa 2007.

Sannan kuma an zabe shi Sanata a karkashin jam’iyyar CPC a cikin 2011 a lokacin da ya kayar da Sanata Ahmed Makarfi bayan Makarfi din ya yi gwamna har sau biyu.

Ranar Alhamis ne Baba-Ahmed ya bayyana wa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Tudun Wada, cikin Karamar Hukumar Zaria cewa ya fice daga jam’iyyar APC.

Ya rubuta masa wasika ne tare da bayyana cewa daga ranar Alhamis din, shi ba mamba ba ne na jam’iyyar APC.

Bai dai rubuta musu dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ba.

Sai dai PREMIUM TIMES ta zanta da shi yau Juma’a ta wayar tarho, inda ya ce ba zai ce ga wani dalili ba, amma dai ya ce idan mutum na son tsira da mutuncin sa, to kada ya dade a cikin APC.

Daga nan sai ya ce a yanke shawarar ficewa daga APC saboda gwamnatin Buhari gwanatin dan dagaji ce, kuma kwamnatin ‘yan wuru-wuru ce kawai.

Da aka tunatar da shi cewa Buhari fa bai boye aniyar sa ta yaki da rashawa ba, sai Baba-Ahmed ya ce “gwamnatin makaryata ce.”

“Da kudin sata aka kafa gwamnatin Buhari, kuma kashi 80 cikin 100 na kudaden da aka kafa gwamnatin APC, daga PDP suka fito. Batun yaki da rashawa kuma da ya ke yi, duk burga ce kawai.

Ya kara da cewa dama can guguwa ce sai kuma hauragiya ta kawo APC ga cin nasara, amma maganar gaskiya ba su da wani shiri.

Ya ce ya koma cikin PDP, domin kashi tamanin bisa dari na ‘yan jam’iyyar APC duk daga PDP suka fito. Idan kuma maganar kashe kasa ne, su ne dai din suka kashe ta a cikin shekaru 18, duk yanzu kuma su na cikin APC.

Share.

game da Author