CUTAR KANSA: Mutane 10,000 ke mutuwa duk shekara a Najeriya – Ministan Lafiya

0

Ministan Lafiya, Isaac Adewole, ya bayyana cewa akalla mutane 10,000 ne ke mutuwa sanadin cutar kansa a kowace shekara.

Ya ce ana yawan mutuwa ne saboda karancin kayan aikin kula da masu cutar ta kansa.

Sai di kuma ya kara cewa a fadin duniyar nan, cutar kansa ta fi tarin TB da kanjamau saurin kashe mutane.

Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da fara aiki da wata na’ura da aka kai Babban Asibitin Tarayya da ke Abuja. A wurin ya kuma gode wa Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Dolapo Osinbajo, kan kokarin da ta ke yi wajen ganin an shawo kan cutar kansa a kasar nan.

Share.

game da Author