Dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP Bode George ya ce cin fuskar da gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike yayi wa ‘yan yankin kudu maso yamma ne yasa ya hakura da takarar da yake yi na shugabancin jam’iyyar.
Za a yi gangamin taron zaben sabbin shugabannin jam’iyyar PDP a Abuja.
Uche Secondus ne dan takarar da gwamnan jihar Ribas yake yi wa aiki.
Wike ya ce a wani hira da yayi wai ‘yan yankin Kudu Maso Yamma wato yarbawa basu tsinana wa jam’iyyar PDP komai ba saboda haka bai ga dalilin bin su ba.
Discussion about this post