Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Turai ‘Yar’Adua ta koma gandun noman wake

0

Cibiyar nan ta Yaki da Cutar Kansa ta uwargidan Tsohon Shugaban Kasa, Umaru Musa ‘Yar’Adua, Turai, wadda aka kashe bilyoyin kudi aka gina, a yanzu an yi watsi da ita, har an koma ana noman wake a ciki.

Turai ‘Yar’Adua ce ta nemi hadin guiwa da Kungiyar IAEA ta duniya a cikin 2009 aka tara bilyoyin kudade daga dadaikun mutane da kungiyoyi tare da tara gudummawar tulin kayan gini da kayan aiki aka kafa cibiyar da ke kan titin Babban Filin Jirgin Sama na Abuja.

Wani bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar cikin Disamba, 2016, ta ruwaito cewa fataken dare sun taba balle cibiyar aka shiga aka kwashe wayoyin kebur na milyoyin nairori.

Ziyarar da PREMIUM TIMES ta kai cibiyar wadda a shekarar da ta gabata ciyawa ta mamaye filin, har yanzu ci gaba aka samu.

Domin a yanzu cibiyar ta yaki da cutar Daji, kansa, ta koma wurin noman wake.

An ware wa cibiyar fadin fili har eka 7.3. A ciki akwai rubabbun kayan aikin da aka bari su ka lalace, ciki har da mita bas-bas guda 200.

A cikin 2008 Turai ta kaddamar da ginin cibiyar inda aka nemi tara gudummawa ta naira bilyan 10.

An tara makudan kudade, amma ba a san ko adadin nawa aka tara ba.

Jami’in tsaron da ke bakin kofar cibiyar ya hana wakilin PREMIUM TIMES shiga ciki. Amma kuma ya nuna takaicin yadda aka bar wurin ya lalace har aka yi asarar bilyoyin nairori.

Da aka tambayi wani jami’in tsaron kuma, sai ya ce jami’an cibiyar kan ziyarci wajen akai-akai.

“Mu na cikin wahala a wurin nan. Ba wuta, kullum a cikin duhu muke kwana. Amma a kulllum jamai’an cibiyar na shaida mana cewa nan ba da dadewa ba Turai za ta farfado da wurin.”

Duk kokarin a ji ta bakin jami’an da ke kula da cibiyar ko wasu majibintan ta ya ci tura.

Share.

game da Author