Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jaddada alwashin da ya dauka na magance Boko Haram a cikin kasar nan.
Da ya ke magana yayin da ya kai ziyara a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Buhari ya ce a matsayin Kano na cibiyar kasuwancin Arewa, a baya Boko Haram sun nemi durkusar da jihar ta hanyar kai munanan hare-haren da suka kawo tasgaro ga harkokin kasuwanci a jihar.
Buhari ya kai ziyara fadar Muhammadu Sanusi II a daya daga cikin wuraren da ya ziyarta, yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar.
Ya kuma kara nanata kudirin gwamnatin sa na magance cin hanci, rashawa da sauran mugayen hanyoyin wawurar dukiyar kasar nan.
Buhari sai ya ce amma nan ba da dadewa ba jihar Kano za ta dawo da martarbar da aka san ta da shi a fannin kasuwanci, fiye ma da abin da aka sani can baya.
Ya na mai cewa hakan kuwa ya biyo bayan nasarar da gwamnatin sa ta samu ce wajen dakile hare-haren Boko Haram.
“Dama gwamnatin mu ta na bai wa abubuwa uku muhimmanci ne fiye da saura, wato kawar da wuru-wuru, samar da tsaro da kuma inganta tattalin arzikin kasa.”
Buhari dai ya bayyana Kano a matsayin tushen dandazon magoya bayan sa, tun daga lokacin da ya shiga siyasa cikin 2002, tare da cewa ya na tutiya da jihar dangane da irin goyon bayan da ta ke ba shi.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarki, ya yaba wa Buhari dangane da ziyarar da ya kai, kuma ya ba shi tabbacin cewa masarautar sa za ta ci gaba da goya masa baya.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba shi shawarwarin da suka dace ta hanyar da ta dace.