Boko Haram sun kashe ma’aikatan UN hudu

0

Boko Haram sun kai wa daya daga cikin motocin sojojin da ke rakiyar wasu ma’aikatan majalisar dinkin duniya, UN kwantan bauna, a Ngala, jahar Barno.

An kai musu harin ne yayin da su ke tafiya kan hanyar su ta rakiyar kai kayan agaji a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Ngala.

An tabbatar da cewa mutane hudu suka mutu sanadiyyar harin. Majiya ta kuma shaida wa PREMIUM TIMES cewa baya ga kisan mutane 4 da Boko Haram ta yi, sun kuma gudu da mutane uku.

Kakakin hulda da jama’a na WFP da ke Maiduguri, Adedeji Ademigbuji, yace biyu daga cikin wadanda aka kashe, direban motar daukar kaya ne da kuma yaron motar daya.

Sai dai kuma WFP ta ki ta cewa komai dangane da wadanda aka ce an sace din su uku.

Ya kuma ce ana nan ana kokarin gano motocin da aka arce da su da sauran ukun da aka yi wa fin karfi aka gudu da su.

Share.

game da Author