Bashin da yayi mini katutu ne ya sa na ke satan yara don in biya – Barayin Yara a Kebbi

0

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya ce sun ceto wasu yara maza biyu masu shekaru 10 da 11 daga hannu wasu barayin yara a jihar sannan barayin na hannu.

Ya ce barayin sun bukaci naira miliyan 2.5 daga iyayen yaran kafin su sako su.

Ya ce sun kama barayin yaran da suka kai 8 ba tare da an biya kudaden fansan su ba a kauyen Dakin Kowa dake karamar hukumar Kontagora jihar Neja.

Kabiru ya ce sun bazama neman yaran ne bayan karan da mahaifin daya daga cikin yaran mai suna Christopher Nnagbo ya kai ofishin su ranar 5 ga watan Disamba.

” Bisa ga wannan bayanai da Christopher ya bamu cewa dan sa mai shekaru 10 ya bace ne a hanyar sa na dawowa gida daga coci a Birnin Kebbi ranar 30 ga watan Nuwamba ya sa muka kitsa yadda zamu gano mabuyar su.”

Kabiru ya ce yanzu haka Christopher ya karbi dan sa sannan suna neman iyayen daya yaron da suka kwato tare da dan Christopher din.

” Ba mu mika yaran ga iyayen su ba sai da asibiti ta tabbatar mana cewa yaran na cikin koshin lafiya.”

Ya kuma yi kira kira ga mutane da su guji karban bashin da ya sha karfin su musamman yadda shugaban barayin yaran ya furta cewa ya fara wannan sa’a ce don ya sami kudin biyan wata bashin da ya ci.

Share.

game da Author