Kotu a garin Kubwa, dake Abuja ta yanke wa wasu maza biyu hukunci bulala biya-biyar saboda satan doya da suka yi a gonar wani mutumi.
Lauyan da ya shigar da karan Babajide Olanipekun ya fada wa alkalin kotun Mohammed Marafa, cewa mai gonar doyan Hyginus Anyandiegwu ya kai karan Habakuk Sunday da Monday Dikko ofishin ‘yan sanda dake Kubwa ranar 21 ga wantan Nuwamba cewa sun sace masa doya.
” Bisa ga rohotan karan da Hyginus ya kai ofishin ‘yan sandan ya ce Habakuk da Dikko sun hada baki sun shiga gonar sa dake Byazin, Kubwa Abuja inda suka saci doya har guda 20.”
Olanipekun ya ce an kamasu ne a kasuwa yayin da suke kokarin siyar da doyar kan Naira 15,000.
Duk da haka lauyan dake kare barayin Moses Ugwumadu ya roki sassauci daga kotun cewa kafin a fara sauraron karan Habakuk da Dikko sun yi tsawon kwanaki 30 a daure.
Daga karshe Habakuk da Dikko sun yi alkawarin yin hannun riga da aikata irin wannan laifin musamman yadda a cewar su wai yunwa ce ta ingiza su ga aikata hakan.
Discussion about this post