Hukumar Kula da Albarkatun mai ta Kasa, NNPC, ta bayyana cewa ko alama babu wani shiri ko tunanin karin kudin man fetur kafin ko bayan bukukuwan Kirisimeti.
A cikin wata takarda da ta raba, hukumar ta bayyana cewa har yau farashin da ake ba dillalan mai a kan naira 133.38 ya na nan, haka farashin gidajen mai na naira 143 ko 145 shi ma ya na nan bai canja ba.
Daga nan sai hukumar ta yi kira ga masu motoci da su yi watsi da duk wata jita-jitar wai za a kara kudin litar man fetur, domin ba gaskiya ba ne.
Sai kuma ta roki masu ababen hawan da su guji sayen fetur su na tarawa ko boyewa, saboda gudun tsada ko karancin da ake yada rudun cewa zai yi.
A karshe hukumar ta ce ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don ganin cewa ba a samu karancin fetur a lokacin bukukuwan Kirisimeti da na shiga sabuwar shekara ba.