Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya ce idan har za a fadi wa kai gaskiya a kasar nan to ba za ko amanta da irin watandar dukiyar kasa da akayi ba lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da sunan biyan kudin rarar mai.
Ya ce an salwantar da sama da naira Tiriliyan 1.3 don haka.
“ Dana tuntubesa kan maganar harkallar da ake yi sai y ace mini, “ Kasan san harkar mai akwai maiko.”
Saraki ya fadi haka ne a wajen taron kaddamar da littafi kan tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan da akayi a dakin taro na Shehu Musa ‘YarAduwa dake Abuja.
Tsohon ministan wasanni a mulkin Jontahan kuma kakakin jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi ya rubuta littafin.
Saraki ya ce Jonathan ba mutum bane da ya damu da sai dole ya ci gaba da zama kan kujerar mulki duk da cewa ya samu mulkin ne ba tare da ya shirya mata ba.
“ A ganina mune da kan mu muke zaban irin shugabannin da za su mulke mu amma Jonathan bashi da wannan ra’ayi na dole sai ya ci gaba da zama a kujeran mulki.
“ Na tuna lokacin ina dan majalisa a majalisar dattijai, na shirya wata kudiri kan fallasa harkallar da akeyi a ma’aikatar mai da irin kudaden da ake wawushewa da sunan kudin rarar mai. Da yake ina jam’iyya mai mulki ne a wancan lokacin sai naga ya dace in sanar wa shugaban kasa abinda ke faruwa kafin in gabatar da wannan kudiri a zauren majalisa.
“ Abin da ya bani mamaki shine bayan na dauki tsawon lokaci ina mishi bayani kan irin abubuwan da ake yi a fannin mai na kasa, ina ganin abin zai tada masa hankali kawai sai ya ce mini “ Sanata ya kamata ka sani cewa shi harkallar mai akwai maiko”, abin sai ya sani cikin dimuwa da zurfin tunani. Amma kuma Shi haka Allah yayi shi. Ba abin da ya dame shi.”
Discussion about this post