Atiku ya yi tir da ayyukan’yan sandan SARS

0

Atiku Abubakar ya bi dimbin ‘yan Najeriya wajen yin tir da halayyar ‘yan sandan musamman wadanda ke yaki da fashi da makami, SARS.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasan ya ce yawan gallazawa da azabtarwa da wadannan ‘yan sanda ke wa ‘yan Najeriya ba shi da wata hujja ko dalili a cikin tsarin dimokradiyya.

“Abin takaici da al’ajabi ne a ce ‘yan sanda wadanda aikin su shi ne kare lafiya da dukiyoyin al’ umma, a ce kuma su ne a gaba wajen gallaza wa jama’a.’

“Na lura da yadda matasa ke yawan kuka da SARS, saboda gallazawar da ake musu. Da an ga matashi da laptop, sai a zaci dan yahoo-yahoo ne. Sai a kama shi a yi ta dukan sa har a illata shi.”

Atiku ya yi wannan bayani ne a jiya lokacin da wani salon zanga-zanga kan intanet ya bullo aka yi ta sukar SARS mai take #End SARS.

Share.

game da Author