Atiku ya caccaki APC a gangamin PDP

1

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar APC da ya fice daga ciki ba su cika alkawuran da suka dauka wa mutanen Najeriya ba.

Atiku ya ce bayan shirga musu karerayi da suka yi sun bisu daya bayan daya suna bugewa.

” In banda Karin talauci da rasa ayyuka da mutane su kayi ta fama da su tsaro ya Kara tabarbarewa a kasar nan.”

Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar PDP za ta karkata akalar Mulki zuwa ga talakawa da mutanen Najeriya.

A jawabin sa, Atiku ya yabawa ‘yayan jam’iyyar Kuma ya yi Kira ga masu zabe da si zabi shugabanni nagari.

Share.

game da Author