Kafin Jam’iyyar APC ta hau mulki, aljanna ce kadai ba ta yi wa talakawan Najeriya alkawari ba. ’Yan bokon cikin ta sun zauna sun rubuta ‘Manufofin Jam’iyyar APC’, ko kuma na ce ‘Kudirorin Jam’iyyar APC.’ A Turance dai sun kira shi da “Manifestos of APC.” Wani kundi ne ko daftari wanda ke dauke da dukkan alkhairan da APC ta yi alkawarin za ta samar wa ‘yan Najeriya idan aka zabe ta ta hau mulki a 2015.
Saukin rayuwa, walwala da rage radadin talauci su ne kan gaba na abubuwan da talaka ke bukata ga gwamnati. A Jamhuriya ta Farko, jam’iyyar NPC mai mulki ta su Sardauna, ta yi bakin jini kamar bakin maciji a zukatan talakawa, saboda abubuwa da dama, amma babba daga ciki shi ne yadda ta fifita ko ta fi bada karfi wajen karbar kudaden haraji daga talakawa.
HARAJI A JAMHURIYA TA FARKO
An rika amfani da Sarakunan Lardi, Hakiman Gundumomi, Dagatan Yankuna da masu unguwannin cikin karkara ana tilasta wa talakawa biyan haraji. An rika kuntata musu, ana tozarta su, har ta kai wanda ya kasa biyan haraji ana kama shi a daure a jikin bishiya ko turke ko gungume itace, a tube masa sutura ana kyara masa ruwan sanyi a lokacin tsananin hunturu.
Wannan ukuba ce ta sa matasa da magidanta suka rika guduwa daga garuruwa da kauyukan su su na tafiya ci-rani. Wani idan ya samo kudin biyan haraji ya koma ya biya. Wasu kuma wannan ce silar fitar su neman arziki a duniya- wasu sun samu sun zama hamshakai, wasu kuma sun bar gida sun shiga duniya sun zama tantirai.
Mulkin Mallaka na Bature shi ne ya fara jaddada karbar haraji a kasar nan. Domin su dama a kasashen su, har yau har kwanan gobe, haraji ne babbar hanyar samun kudin shiga ga gwamnatocin su.
Tunda ba su da albarkatun kasa wadanda ake sayarwa a samu kudaden shiga, irin su danyen man fetur da sauran ma’adinai kamar zinari da sauran su.
Da kudaden haraji suka raya kasashen su har suka yi mana nisa fintinkau. Domin su duk abin da ya shiga aljihun gwamnati, to ya shiga kenan, ba a sacewa, bai yiwuwa shugabanni su wawuri dukiyar gwamnati.
TSAKANIN AMINU KANO DA BUHARI
Marigayi Malam Aminu Kano ya yi tasiri a zukatan talakawan Arewacin kasar nan, tun daga Barno, Bauchi, Fataskuman, Damaturu, Kano, Katsina, Zaria, Gusau, Funtuwa, Kaura Namoda, Gusau, kai har Sokoto, ba don komai ba, sai yadda ya rika amfani da siyasar sa ya na yaki da yadda ake gallaza wa talaka, musamman yadda ake karbar haraji da jangali da karfin tsiya. Shi ya sa lokacin da jam’iyyar sa PRP ta kafa gwamnati a Jihohin Kano da Kaduna a zaben 1979, farkon abin da ta fara yi shi ne soke haraji da jangali.
Muhammadu Buhari ya samu irin farin jinin da Malam Aminu Kano ya samu a Jamhuriya ta Farko da ta Biyu. Jam’iyyar sa APC ta zo cike da alkawurran samar wa talakawa ingantacciyar rayuwa mai sauki sabanin irin wadda ake ciki a karkashin jam’iyyar PDP kafin zaben 2015.
Ajanda ta 14 daga cikin alkawurran da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya domin a zabe ta, shi ne alkawarin rage dogaro da ribar danyen man fetur da gas.
Amma a karkashin wannan ajandar, babu inda jam’iyyar ta rubuta cewa za ta bullo da hanyoyin tara kudaden haraji barkatai domin a rika samun kudaden shigar da za su maye gurbin na danyen man fetur, ko su kara wa ribar danyen mai yawa domin a yi wa al’umma ayyukan raya kasa.
APC: JAM’IYYAR HARAJI
Kwanan nan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa babu mafita sai dai ‘yan Nijeriya su ci gaba da shan wutar lantarki da tsada, domin ribar danyen man fetur ta kure da kuma wasu dalilai da ya bayar wadanda babu su a cikin ajandar jam’iyyar APC. Har ma cewa ya yi babu makawa nan gaba sai an kara kudin wutar lantarki, amma dai a yanzu za a daure a ci gaba da sha a cikin tsadar da mu ke kuka a kan ta.
Kudin hasken lantarki ya nunka, ya rubanya kuma ya maya a lokacin gwamnatin APC fiye da lokacin gwamnatin PDP.
Tsakanin watannin Oktoba da Nuwamba na wannan shekarar, ko gidan biki Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta je sai ta bayyana cewa ribar danyen man fetur bai isa a tafiyar da gwamnatin Nijeriya da ita ba. Don haka tilas sai an kirkiro hanyoyin samun kudaden shiga daga ‘yan Nijeriya ta hanyar haraji. Ga hanyoyin nan kuwa barkatai sai fito da su ake ta yi, wasu an fara, wasu kuwa ana shirin farawa gadan-gadan.
Kwanan nan an dauki jami’an tara kudaden haraji ga gwamnatin APC, kuma tuni har an tura jami’ai 1,710 a cikin jihohin kasar nan. Aikin da za su fara yi shi ne su rika wayar wa jama’a kai dangane da muhimmancin biyan haraji. Amma an ba su wa’adi wanda daga wannan ranar duk wanda bai biya na baya ba, ko ya ki biyan na gaba idan lokacin biyan ya zo, to ya aikata babban laifi ga gwamnatin APC. A manufofin APC babu wannan batu ko makamancin sa.
HARAJIN ‘TOLL GATE:’
A shekarun baya an rushe manyan shingayen da aka yi kan titi daidai shiga manyan birane da nufin tara kudaden shigar da ake aikin gyara ko gina tituna da su. An yi ta sukar wadannan shingaye saboda yadda ake tatsar kudade ga masu motoci, ta yadda idan mai mota ko motar haya za ya wuce sau goma, to sau 20 direba zai biya haraji kenan, a zuwa da kuma komawa.
Sannan kuma an rika sukar tsarin saboda yadda ake ganin ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati ne ke sace kudaden ribar da ake tarawa daga danyen man fetur, a gefe daya kuma ana gallaza wa ‘yan kasa da karbar harajin ‘toll gates.’
A yanzu gwamnatin APC za ta dawo da tsarin gina wadannan shingaye ana karbar kudade a hannun direbobin motocin haya da masu motocin kan su. Idan ka na Kaduna, ba za ka je Zaria sai ka biya kudin harajin ladar fitar ka Kaduna za ka Zaria. Haka idan ka dawo daga Zaria, ba za ka shiga gidan ka a Kaduna ba, sai ka biya gwamnatin APC ladar shigar da za ka yi a gidan ka. A ina aka yi haka da APC a cikin ajandar alkawurran da ta yi wa talakawa kafin a zabe ta?
Farkon wannan makon da ya gabata, Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, mazauna Abuja za su rika biyan harajin ladar zama babban birnin tarayya, wanda da wannan harajin ne gwamnati za ta rika gina ababen more rayuwa da ci gaban kasa a Abuja. Minista Mohammed Bello ya ce maganar gaskiya kudin shigar da gwamnati ke samu ba su kai a rika gudanar da ayyuka kamar gina titina da sauran su a Abuja ba. Shin dama akwai wannan tsarin a cikin ajandojin APC wanda ta yi kamfen da su kafin a zabe ta?
Da wane haraji gwamnatin PDP ta gyara Abuja a cikin shekaru 8 da suka gaba ta? Wa da wa PDP ta yanka wa haraji da fadada titin Abuja zuwa Zuba? Daga haraji ne PDP ta tara kudin da ta fadada titin Abuja zuwa Gwagwalada?
Kafin hawan APC an gina sabbin manyan gadoji a cikin Abuja da kewayen ta fiye da 20. An gina titina da suka hade birnin Abuja da unguwannin da ke kusa da birnin, sama da 30. Shin su ma da tatsar kudin haraji aka gina su?
WAHALA A GWAMNATIN APC: ‘Duk cikin aikin ne.
A bar dan Nijeriya da abin da ya ishe shi mana. APC ta hau gwamnati a lokacin da ake canja Dalar Amurka Naira 180. A yau Dala 1 a kan naira 360. Kuma shikenan har abin ya zama jiki. Litar man fetur ta koma naira 145, daga naira 86 kafin hawan APC. Mutum ba zai fahimci illar ba, sai ya yi kwana da kwanaki ya na tara kudin sayen buhun shinkafa, amma ya na ji ya na gani zai ce a dai auna masa kwano biyar kawai. Amma fa a wurin wanda ba ya so a fada wa APC gaskiya, to duk abin da gwamnatin Buhari ta yi, ‘ai duk cikin aiki ne’, wai mai gona ya mari dan kodago.
Idan aka koma jihohi, za mu ga cewa gwamnonin su ba su da amfani sai kowane wata su jira kason gwamnatin tarayya kawai. Babu jihar da ke iya biyan albashi sai ta jira kudi daga gwamnatin tarayya. Sun kasa kirkiro hanyoyin samun kudi wanda kowa zai amfana. Sai dai idan yau talaka ya shiga adashe ya tara kudi ya sayi Keke NAPEP. To shikenan gwamnatin jiha ta samu saniyar tatsa, sai a kafa masa hukumar karbar haraji iri daban-daban.
Gwamnoni APC basu da bamabanci da gwamnonin PDP kafin saukar gwamnatin Jonathan. Domin watanni biyar kafin saukar PDP, sai da aka rika ciwo bashi an aba su, suna biyann albashi. Sun ma gwamnonin jam’iyyar APC tun tafiya ba ta yi nisa ba, ba su iya biyan albashi duk da kudin kasafin karshen watan da ake ba su, sai sun jira daga kudaden Paris Club. To ranar da na Paris Club suka kare fa? Sain kaka?!
An wayi gari hatta zaman Abuja din nema ya ke ya gagari wadanda ba daga aljifan gwamnati su ke kamfata su ke ci da sha da wandaka ba. Kama hayar shagon sayar da abinci ko sayar da kaya a tsakiyar birnin Abuja sai ka biya kudin hayar sheakara daya daga milyan uku abin da ya yi sama.
Shago a Kasuwar Wuse, wanda bai kai fadin ban-dakin gidan haya a Kano ba, sai a ce maka naira milyan biyu a shekara. A Nijeriya fa ba a Los Angeles ko Washington ba. Duk lokacin da muka yi wa ‘yan kasuwar nan magana, sai su ce ai haraji su ke biya iri daban-daban. Kuma gwamnati na kallo. Tunda an sa wa kowa ido, an kyale shi, don me rayuwa ba za a ta yi tsada ba? Don me ba za a rika satar kudin gwmanti don a ci gaba da rayuwa a Abuja ba?
Idan ka shiga shagon saida abinci, rasidin da za a ba ka za ga a akwai harajin gwamnatin tarayya, akwai wani harajin ma, kai har da harajin ladar zaman da ka yi a cikin shagon ka ci abincin. Idan ka ce dauka za ka yi ka ci a gida, shi ma akwai wannan harajin daban. Kai jama’a!
TUNANIN APC DABAN, NA TALAKA DABAN
Babban abin da talakan kasar nan ya yi tsammani gwamnatin APC za ta fara yi, shi ne ta dukufa ta kwato tiriliyoyin nairorin da APC din ke cewa an sace, sai hana manyan ma’aikatan gwamnati satar kudaden Nijeriya, sannan sai an fara daure wadanda ake cewa sun yi satar, sannan sai a kirkiro hanyoyin da za a yi amfani da kudaden da aka kwato.
Amma har yau ba a kwato abin da ya taka kara ya karya ba. Ba a daure ko da tsohon kansila ko Sanata ko Gwamna ko daya ba. Tambaya su ke ta yi wai ina kudaden da ake cewa an kwato? Da yawan wadanda ake zargi da wawurr kudden sun narke a cikin jam’iyyar APC. Sannan kuma asusun bai-daya, wato TSA da ake tutiyar ana amfani da shi, bai hana manyan ma’aikatan gwamnati satar kudade ba, sai kuma a rika kirkiro hanyoyin gallaza wa al’umma?
Masu kuka da wannan tsari da gwamnatin APC ta shigo da shi, su na ganin cewa, tun da an ce ribar danyen man fatur ta yi wa kasar nan kadan, to a rage albashi da alawus-alawus na gwamnoni mana. A zabtare bilyoyin kudaden da ake kashe wa ‘yan Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa mana.
A daina bai wa gwamnoni kudaden ‘tsaro na ko-ta-kwana, wato security vote mana. A hana kowane dan siyasa fita bulkara kasashen waje mana.
Shi kan sa Shugaban Kasa ya rage yawan tafiye-tafiye mana zuwa kasashen waje. A hana gwamnoni zuwa China ciwo basussukan da ba gwamnatin su za ta biya ba mana.
Gaba daya gwamnatin APC nema ta ke ta manta da komai, saboda ta maida hankalin ta wajen kakaba wa ‘yan Nijeriya haraji.
Da za ka dauki ajandar jam’iyyar APC ka karanta alkwaurran da ta daukar wa ‘yan Nijeriya wadanda aka watsar aka mata da su, da abin zai ba ka mamaki.
Ka dauki ajandar hana cin hanci da rashawa ka karanta tanadin da aka wa ma’aikacin da gwamnatin APC ta kama da almundahana, sannan ka kalli yadda kiri-kiri aka bar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi tafiyar sa, to dariya kawai za ka yi, sannan ka jefar da daftarin ajandar. Ko kuma haushi ya kama ka har ka kekketa shi.
Watakila dai gani aka yi tunda wadancan alkawurran ba saukakkun ayoyi ko hadisai ba ne, gara a yi watsi da su, haraji kawai shi ne mafita.
Mu gani mu fada shi ne aikin mu. Amma Bahaushe ya ce, “zomo ba ya fushi da makashin sa, sai maratayin sa.
Tun daga shafin gabatarwar daftarin kudirorin APC aka fara baro bida baya. A shafin gabatarwar, Shugaban Jam’iyyyar, John Odigeie Oyegun ya yi bayanai, ciki har da inda ya ke cewa: “Za mu gaggauta tabbatar da aiwatar da shirin nan na amfani da takardar kudi ta bai-daya a tsakanin kasashen Afrika ta Yamma.”
Tun daga ranar da APC ta hau mulki zuwa yau, ba na jin Oyegun ya je ko nan da Wagadugu,ballantana batun samar da takardar kudi ta bai-daya a Afrika ta Yamma.
Bari dai na tsaya haka nan, kada ni ma a kakaba min harajin kasa yi wa alkawurran APC tankade da rairaya nan gaba, ba jimawa ba.
Discussion about this post