An yi garkuwa da mutane hudu a Jihar Neja -Inji ’Yan sanda

0

Rundunar ’Yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane hudu a kauyen Zazzaga da Masuku da cikin jihar.

Kakakin riko na rundanar jami’an tsaron, ASP Peter Sunday ne ya bayyana haka a wata takardar da ya fitar ga manema labarai, a Minna.

Ya ce wadannan kauyuka biyu su na cikin Karamar Hukumar Munya da Shiroro ne.

Sunday ya ce masu garkuwar sun kuma kashe wani jami’ain dan sanda daya mai suna Sule Danjuma, wanda ya yi kokarin hana maharan su gudu da wadanda suka yi garkuwar da su, a lokacin da suka gudu da mutane biyu a kauyen Zazzaga.

Ya bayyana sunayen ’yan matan da aka gudu da su a kauyen Masuku da sunayen Shekto Ali da kuma Mai’aba Shehu.

Ya ce sun baza jami’ai a cikin farin kaya su na kokarin ceto su, kuma su na neman gudummawar jama’a idan an ji kishin-kishin to a sanar da su.

Share.

game da Author