AN SHIRYA: NPA ta umarci a dawo wa Intels duk kwangilolin da ta ke yi a tashoshin ruwan kasar nan

0

An sasanta tirka-tirkar da ta ki ci, ta ki cinyewa tsakanin Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa, NPA da Intels, kamfanin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Sabani ya shiga tsakanin su bayan da su ka kasa cimma yarjejeniyar yadda Intels zai rika tara kudaden harajin da ya ke karbar wa Gwamnatin Tarayya a manyan tashoshin jiragen ruwan na Najeriya.

NPA dai sun shar’anta wa Intels bin tsarin asusun bai daya, wato TSA. Ma’ana, duk kudaden da Intels ke tarawa, ta rika zubawa a Asusun Bai Daya, (TSA) a Babban Bankin Najeriya.

Intels ya ce idan aka ce su rika tara kudi a CBN, sannan daga baya a raba riba, to kusan gaba daya aikin na su tsayawa zai rika yi, domin CBN ba za ta rika ba su rancen kudi ba.

Wannan kiki-kaka ce ta kai ga har aka soke yarjejeniyar kwangilar tara kudaden harajin da Intels ke yi a tashoshin manyan jiragen ruwa a kasar nan.

Masu lura da siyasar Najeriya na cewa wannan ma na daga cikin dalilin da ya sa Atiku ya fice daga APC, ya koma shekar sa ta farko, wato PDP.

A wata takarda da ta fito daga hukumar kula da tashoshin, wadda shugabar hukumar, Zainab Usman ta sa wa hannu, ta bayyana cewa an sasanta da Intels, zai ci gaba da aikin sa.

Ta ci gaba da cewa ta kuma aika da takardar sanar da Ministan Shari’a cewa za a iya janye soke kwangilar da aka yi, tunda Intels ya bada hakuri cewa zai bi doka.

Share.

game da Author