Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Terna Tyopev ya ce an sako shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Damishi Sango.
Ya sanar da haka ne wa PREMIUM TIMES da safiyan yau Litini bayan ya aika da sakon wayan taraho (text message).
” Na sami tabbacin haka ne daga wajen jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna’’
Wani cikin ‘yan uwan Sango wanda ya bukaci a boye sunnan sa ya ce an sako Sango tare da sauran mutane 4 da aka sace din a dare jiya Lahadi.
Shima sakataren jam’iyyar PDP na jihar Filato John Akans ya tabbatar da haka.
Sai dai babu wanda ya tabbatar ko an biya kudaden da ‘yan garkuwan suka bukata kafin aka sako su.
Discussion about this post