An sace tsohon Sanata, an ce sai an biya naira miliyan 80

0

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da Sanata Ayo Arise, tsohon sanatan jihar Ekiti.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da shi ne a yau Litinin da sanyin safiya a kan hanyar sa ta zuwa Abuja.

Har yau PREMIUM TIMES ba ta gano ainihin inda aka sace shi din ba, ko a cikin jihar Ondo ko kuma a jihar Ekiti ne.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Ekiti, Alberto Adeyemi ya tabbatar da sace sanatan, amma ya ce ba zai iya kara yin wani bayani ba, domin ba shi da hurumin kara cewa komai.

Amma kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa wadanda su ka yi garkuwa da sanatan su na neman sai an biya su tsabar kudi naira milyan 80 kafin su sake shi.

Share.

game da Author