An yi asarar rayuka a wata gabzawa da aka yi tsakanin jami’an ’yan sanda da masu hakar ma’adinai a jihar Taraba.
Kakakin yada labaran ‘yan sandan jihar, David Misal, ya tabbatar da faruwar rikicin wanda ya faru jiya Alhamis, a Mayo Sine da ke yankin Mambilla, cikin Karamar Hukumar Sardauna.
Dama da dubban masu halar ma’adinai ne ke hakar albarkatun kasa a wurin tun sama da shekaru 10 da suka gabata.
Wata majiya a karkarar da abin ya faru, ta ce ‘yan sanda ne dauke da makamai suka yi wa wurin dirar mikiya, da nufin su fatattaki duk wani wanda ke wurin, to amma sai suka hadu da cirjiyar wadanda aka je a kora din.
“Yayin a jami’an tsaro suka isa, sun tarwatsa ‘yan bukkokin nan na a-taru-a-kwana, wanda masu hakar ma’adinan ke kwana a ciki. Sannan sun kwace kayan da masu hakar ke amfani da su suna hahar.’’ Inji wani mai suna Hammadu Bello. Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Wato a baya an mallaka wa wani kamfani na kasashen waje wannan fili inda gungun jama’ar ke cin kasuwar su ta hakar ma’aidinai. Amma sai su mutanen da ke hakar su ka ki tashi daga wurun duk da an rigaya an damka a hannun wanil. Dalilin da ya sa jami’an tsaro zuwa kenan domin su fatattake su.
Wani mazaunin wurin mai suna Joseph, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu hakar ma’adinan sun fusata su ka kori jami’an tsaron kuma suka bankawa kayan wannan kamfani na kasar waje wuta.
“ Wurin kokarin kwantar da tarzoma ne, ‘yan sanda suka bude wuta, suka kashe da dama kuma suka jikkata wasu masu yawa.
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da harin da aka ce an kai wa jami’an su, amma ya ce bai kammala binciken yadda aka yi ko yawan wadanda suka rasa rayukan su ba.