An nada wa Hukumar Kula da Hada-hadar Kudade, SEC, Shugaban Riko

0

A yau Litinin ne aka nada wa Hukumar Kula da Hannayen Jari ta Kasa, SEC, shugaban riko, mako guda bayan dakatar da Darakta Janar na hukumar, Munir Gwarzo.

SEC, ta bada tabbacin cewa ba za ta bari kasuwar hada-hadar hannayen jari ta fada jula-jula ba, shi ya sa ta gaggauta nada sabon Darakta Janar, amma na riko, mai suna Abdul Zubair.

Bincike ya nuna cewa an dakatar da Gwarzo ne saboda ya ki amincewa ya dakatar da binciken harkallar da ta dabaibaye kamfanin mai na Oando, wadda ya fara yi.

Oando dai na shan suka da kuma yawan rubuta korafe-korafe a kan sa, wanda hakan ya sa Munir yin binciken.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeoasun ta dakatar da Gwarzo a farkon makon da ya gabata.

Yayin da a gefe daya ake zargin sa da kamfatar naira milyan 104.85 a matsayin kudin sallama, alhali bai yi ritaya ba, sai kuma wasu kwangiloli da aka yi zargin ya baiwa kamfanin da ya ke da hannun jarida a ciki, watp Medusa Investment Ltd.

An dakatar da shi ne tare da wasu jami’an hukumar biyu.

Gwarzo dai ya ce kudin da ya cira na sallama, na tsohon aikin sa da ya yi kuma ya sauka ne, kafin a nada shi shugaban SEC.

Share.

game da Author