Kwamishinan harkokin mata na jihar Katsina Badiyya Hassan ta ce tsakanin shekarar 2011 zuwa 2017 jihar ta tallafa wa mata 479 ta hanyar basu horo da koyar dasu wasu sana’o’in hannu.
Ta fadi haka ne a taron yaye wasu mata da gwamnati ta horar ranar Talata.
Badiyya ta ce cikin sana’o’in da aka koya wa matan sun hada da hada takalma, hada jakunkuna, saka, yin sabulu, manshafawa da turarai.
Ta kuma kara da cewa bayan an kammala koyar dasu gwamnatin za ta raba wa kowanen su jarin Naira 5,000 sannan za su raba kayan aiki wa mata 21 wanda suka fi kokari daga cikin su.
Shugaban daya daga cikin makarantun koyar da sana’o’in hannu dake jihar Fatimah Mohammed tayi kira ga gwamantin jihar da a karo musu kayan koyar da daliban.
Discussion about this post