Hausawa sun ce “in da rai ai shekara kwana ce.” Kamar jiya ne muka shigo 2017, ga shi har ta kawo karshe, nun fara jin kamshin 2018.
A kan haka, PREMIUM TIMES HAUSA ta rika kawo wasu matsalolin da su ka dabaibaye gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, aka kasa magancewa a 2017, wadanda za a yi dakon jigilar su zuwa sabuwar shekara:
1. MATSALAR MAN FETUR:
Da yawan wadanda ke cikin wannan gwamnati, ciki kuwa har da Shugaba Muhammadu Buhari, da su aka yi ‘jihadi’ da jidalin yaki da gwamnatin Goodluck Jonathan, a cikin watan Janairu, 2012, yayin da gwamnatin ta yi sanarwar karin kudin fetur.
An shafe makonni ana zanga-zangar rashin amincewa da cire tallafin mai. Lokacin da Gwamnatin Buhari ta hau, ta rasa yadda za ta yi da matsalar fetur, har sai da ta kai ga yin karin da kan ta, wato cire tallafin.
A lokaci daya an yi kari daga N86 zuwa N145 a kowace litar man fetur. Magoya bayan wannan gwamnatin sun yi kirarin nuna cewa wannan kari tamkar wani sadaukar da rayuka da dukiya ne don a gyara Nijeriya.
Ministan Mai Ibe Kachukwu da kan sa ya ce kafin wata shida farashin man zai fado kasa warwas. Sai dai kuma a yau an wayi gari saboda matsalar fetur ana saida lita daya har naira 400. Abin mamaki kuma Buhari shi ne Babban Ministan Fetur.
Idan ba a manta ba, kafin ya hau mulki, Buhari ya rika caccakar rashin iya mulkin Jonathan, ya na cewa N45 ya kamata dan Nijeriya ya rika sayen litar fetur daya.
2. CIN HANCI DA RASHAWA:
Duk da yadda ake karade kafafen yada labarai da labaran karbe kudade daga kadarori, har yau ga shi ana neman shiga 2018, amma har yau kotu ba ta daure ko da barawon kudin gwamnati guda daya daga cikin manyan ‘yan siyasa ba.
Tun daga kan Shugaba Buhari har alkalan har sauran fannonin tsaron kasa, kowa Na shan zargi daga jama’a cewa harkar yaki da cin hanci da rashawa ta na nema ta zama tatsuniya.
Irin yadda Buhari ya rika kak-kare tsohon Sakataren Gwamnati, Babachir Lawan da kuma yadda har yanzu an kasa hukunta shi, bayan an kore shi, ya sa da yawa sun rika jefa wa Buhari alamomin tambaya.
Su kan su jami’an tsaro, an ga yadda DSS da NIA suka hana EFCC ta kama tsoffin shugabannin su, wadanda duniya ta ji labarin yadda su ka shiga harkallar kudade.
Abin da ya fi bai wa jama’a mamaki shi ne yadda Fadar Shugaban Kasa ta nuna kamar ma ba ta san hakan ya faru ba.
Wani abin takaici kuma shi ne, had yau dai ba ta canja zani ba a fannin manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya, masu takara da tseren wawure kudaden gwamnati.
Wani rahoto da wata jarida (ba Premium Times) ba ta buga a karshen makon nan, ya nuna cewa bincike ya tabbatar da ma’aikatan gwamnati na wawashe kashi 60℅ bisa 100% na harajin da ake tarawa.
3. TATTALIN ARZIKI:
Tun daga hawan wannan gwamnatin har zuwa yau, iyakar kure malejin tunanin ci gaba a Nijeriya shi ne ‘abinci’, ‘abinci, ‘abinci.’ Babu wani tunani daga masara sai shinkafa da kuma yadda za a rika sarrafa su a ci.
Lokacin da Buhari ya hau mulki, ana sayen Dalar Amurka naira 220. Amma tun da 2017 ta kama, har yau ga shi za a shiga 2018 ana canjar Dala daya sama da naira 360.
4. RIKICE-RIKICE DA KASHE-KASHE:
Gwamnatin Buhari ta gaji mumanan rikice-rikice daga lokacin gwamnatin Jonathan. Duk da dai ta dakile bazuwar Boko Haram a Arewacin kasar nan, har yau da sauran eina a kaba a jihohin Barno da Arewa-maso-Gabas a wasu wurare.
Hare-haren Barayin Shanu a Zamfara da Katsina da Kaduna ya kara munana sosai tare da kashen daruruwan Fulani bayan an kwace musu shanu.
Fadan Fulani Makiyaya da masu gonaki ya tsananta a 2017. Haka nan kuma yawaitar sace mutane ana garkuwa da su, ta fi tsananta a 2017.
Dukkan wadannan babu wata alama ta shawo kan su a 2017, sai ma dakon su a kai zuwa cikin 2018 da za mu yi nan da makon daya.
5. SAMAR DA AIKIN YI:
Kafin APC ta hau mulki, ta yi alkawurra da dama na samar da ayyukan yi ga matasa. An alkawarin samar wa milyoyin matasa aiki a cikin wannan zango na 2015 zuwa 2019.
Ga shi kwanaki kadan ya rage a shiga shekara ta uku da mulkin APC, amma an maida hankali ne ga aikin N-Power, wanda shi ma ko a wannan shekara da ake ganin an dauka da yawa, ba su kai mutum 500,000 ba.
Said kuma gashi a karshen Dusamba din nan, kididdiga ta nuna cewa wadanda suka rasa aiki a Nijeriya, a cikin 2017, sun kai milyan 4.
6. MATSALAR FANNIN ILMI:
Za a shiga sabuwar shekara ta 2018 dauke da dakon wata gagarimar matsalar ilmi. Idan za a iya tunawa, gwamnatin APC ta yi alkawarin gyara matsalolin fannin ilmi idan ta hau mulki.
To wata babbar matsala kuma ita ce yadda a cikin 2017 ta bayyana cewa daga cikin daliban da za su kammala sakandare, kashi 30℅ ne kadai daga cikin kashi 100℅ za a iya dauka zuwa jami’o’i.
Kenan ko yaron ka ya ci jarabawa, tsugune-tashi bai kare ba, tunda ba shi da tabbas na zarcewa jami’a.
Lokacin da APC ta hau mulki, an yi tunanin tun daga kan kansila har kwamishinoni da gwamna kowa zai nuna kishin gyaran ilmi, musamman a Arewa inda aka tsere mana fintinkau.
A tunanin wasu masu zabe, shugabannin za su cire ‘ya’yan su daga makarantun kudi su maida su Na gwamnati, domin a gyara harkar ilmi. Amma hakan bai samu ba.
Kama daga kansila har kwamishinonin ilmi, duk ‘ya’yan su makarantun kudi su ke zuwa ba na gwamnati ba. Ta yaya za a gyara ilmin firamare a matakin farko?
Wasu jami’an kula da harkar ilmi sun maida gina ajujuwa da yi wa tsoffin gine-ginen makarantu fenti tamkar shi ne ci gaban fannin ilmi.
Cikin Yuli, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo wani rahoto kan matsalar ilmin firamare a Arewa, har ta bada labarin wani malamin firamare da aka dauka aka tura a wata makaranta cikin Kura, jihar Kano.
Malamin ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa da ya je makarantar a cikin 2017, shekaru biyu bayan hawan APC mulki kenan, sai da ya koya wa dukkan ‘yan aji 4 yadda za su rika rubuta sunayen su da na mahaifan su. Kafin zuwan sa ya ce duk ba su iya ba, kuma a aji daya akan samu yaro har sama da 120.
7.MATSALAR KASUWANCI:
A cikin shekara uku na mulkin APC, harkokin kasuwanci sun shiga garari, ta kai hatta mai saida tuwo-tuwo ko mai kosai idan an yi mata korafin cewa kayan ta ya yi tsada, sai ta ce, “ai Dala ta tashi.” Dala dai a cikin 2014 naira 190 ake sayar da ita, yanzu kuwa har N360.
A yau, irin yadda gwamnatin APC ta gigice wajen kirkiro hanyoyin tara kudaden haraji, abin ya yi yawa sosai, kuma a kan talakawa da ‘yan kasuwa abin ke karewa. Domin su ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa, duk daga aljihun gwamnati su ke yin dukkan wandaka da wasirar da su ke yi.
Ko yanzu ana nan ana kokarin kafa dokar yi wa direban mota tarar naira dubu 100 idan ya karya dokar tuki, kamar tsallaka fitilar kan titi kafin a ba shi hannu ko kuma a kama shi ya na tuki kuma ya na amsa wayar selula a lokaci guda.
Har yanzu komai daga waje ake shigo da shi, ba a yi wani kwakwaran gyara da zai bayar da kariya ga jarin ‘yan kasuwa da masu sha’awar kafa masana’antu a kasar nan ba. Su kan su masu dan kokarin kafawa din, duk masana’antun kayan abin da za a ci ne kawai su ke yi, ba abin da zai kawo wa kasa fifikon zama wata mashahuriya ba.
8. MATSALAR MANYAN AYYUKA:
Cikin makon da ya gabata Gwamnatin APC ta cika kasar nan da labarin bayar da kwangilolin aikin tituna. Da yawa na ganin abin da wahalar gaske ya dore ko ma ya tabbata a wadansu wuraren, domin babu kudin a kasa da za a gudanar da ayyukan. Sannan kuma ba ayyuka ba ne da za a kammala a cikin shekara daya.
Wata matsala kuma da ‘yan Arewa ke kuka da ita shi ne duk wasu manyan ayyuka na Arewa, ba a kirkire su ba, sai yanzu da gwamnati ta shiga shekara ta uku. Amma duk wani abin da za a yi a Lagos, daga wadanda aka kammala, sai wadanda ake kusa da kammalawa.
Aikin lasken lantarki a Mambilla kwanan nan aka bayar da shi. Ga aikin jirgin kasa zuwa Kano daga Lagos, aikin titin Abuja zuwa Kano da wasu ayyukan da wasu ke kallon duk babu tabbas na kammala su a nan kusa.
Akwai aikin gina wasu titina 25 da gwamnatin APC ta bayar da kwangila da za a gina a karkashin tsarin karbar kudade na tsarin musulunci, mai suna “SUKUK.”
Abin da jama’a da dama ba su gane ba, shi ne ba gwamnati ce za ta yi aikin da ribar danyen man fetur ko wasu kudi na ta ba, a’a.
Gwamnati za ta fanshe wadannan naira bilyan 100 na “SUKUK” ne daga tashoshin karbar haraji a hannun kowane direban mota da za a rika karba, wato “Tollgates.”
A baya ‘yan Nijeriya sun yi korafi an cire “tollgates”, yanzu kuma gwamnatin APC za ta sake dawo da su domin a rika tatsar kudade daga hannun masu motocin hawa da na haya.
Idan direba ya dauki fasinja daga Kano zuwa Abuja, sai ya biya kudi akalla wurare uku a zuwa, wurare uku a komawa. Ga kuma tsadar fetur wanda a da ya ke saya N87, an maida shi N145. Shin akwai wanda ya isa ya hana direba kara wa fasinja kudin mota?
9.MATSALAR KASAFIN KUDI:
‘Yan Nijeriya da dama na ganin laifin Majalisar Tarayya musamaman idan su ka ki sa hannu da wuri kan kasafin kudi da Shugaba Muhammadu Buhari ke gabatarwa.
Sai dai kuma akwai abubuwan dubawa sosai. Su na biciko asarkala da zure da barankyankyama a cikin kasafin yawancin ma’aikatu sosai.
A cikin makon da ya gabata, mun ga yadda Karamin Ministan Ayyuka ya kwashi buhun kunya a Majalisar Dattawa, lokacin da ya wakilci Ministan Ayyuka, Raji Fashola wajen kare kasafin kudin ma’aikatar ayyuka.
Kiri-kiri Majalisar Tarayya ta gano yadda aka yi dafkaren naira bilyan 16, wadanda majalisar ta ce sau biyu su ka fito a wurare daban-daban, alhali kuma duk ‘dodo daya za su yi wa tsafi.’
Haka tilas ministan ya tashi daga gaban kwamitin majalisar dattawa ba tare da ya iya yin wani kwakkwaran bayani ba.
Sannan kuma malajisar dattawan ta ce har yau Gwamnatin Buhari ba ta yi ayyukan da su ka kai kashi 50 cikin 100 ba, daga kasafin 2017, ga shi kuma ta tura kasafin 2018 a majalisa ta na so a amince da shi.
10. RUDANIN SABBIN JAM’IYYU:
A karkashin wannan gwamnati, ana ta tilasta wa hukumar zabe na yi wa jam’iyyu barkatai rajista. Ta kai yanzu jam’iyyu sun doshi 67. Ana sa ran kuma cikin 2018 za a yi wa wasu da su ka haura 30 rajista.
Idan aka lura da yadda INEC ke aiki a yanzu a tsanake wajen tabbatar da gudanar da tsabe kan ka’ida tare da saisaita turbar dimokradiyyar kasar nan, bai dace a nemi dagula wa INEC aiki ba, ta hanyar dora wa hukumar nauyin kula da jam’iyyun siyasa kusan 100.
Da me INEC za ta ji? Da aikin shirya zabuka ko bibiyar jam’iyyun siyasa? Da aikin tantance ‘yan takara a jam’iyyu kusan 100 ko kuma da aikin samar da takardun dangwala kuri’a mai dauke da jam’iyyu barkatai? Me ya sa za a shigo da tulin jam’iyyu a karkashin wannan mulki na APC? Wane tasiri za su yi a zabe?
Kada fa a dagula kyakkyawan matakan da INEC ta dauko ta na gudanar da zabuka a kan tsarin da ake sam-barka.
Discussion about this post