An karo taragon jirgin Kasa 10 don jigilar matafiya daga Kaduna – Abuja

0

A yau Alhamis ne manajan tashar jirgin kasa dake Idu, Victor Adamu ya ce hukumar kula da tashoshin jiragen kasa ta Najeriya NRC ta karbi taragon jiragen kasa 10 da wadanda suke daukar manyan kaya guda biyu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja Adamu ya ce za a kaddamar da su ne a watan Janairu na 2018.

Ya ce manyan taragon da za su dunga daukan mayan kayan na ajiye a tashar jirgi dake Idu.

” Za a yi amfani da tarago biyar da wanda ke daukan manyan kaya daya a tashar Rigasa daya a nan Idu.”

Daga karshe manaja Adamu ya bayyana Jin dadin sa ga wannan himma da gwamnati ta yi.

Share.

game da Author