Hukumar tsaro na Civil Defence NSCDC ta kama wasu mazaje 5 da laifin yi wa yara kanana fyade a Mubi jihar Adamawa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Suleiman Baba ya sanar da haka wa manema labarai a Yola.
Baba ya ce mazajen da suka kama sune, Abdullahi Ibrahim mai shekaru 32, Musa Mohammed mai shekaru 31, Bakura Mohammed dan shekara 39, Joseph John shima mai shekaru 29 da Mohammed Musa mai shekaru 42.
Ya ce gwajin da aka yi wa yaran ne wanda dukkan su ba su wuce shekaru 10 zuwa 12 ba a asibiti ya kara tabbatar da abin da suka aikata.
Baba ya ce za su maka mazajen a kotu bisa ga laifin da suka aikata sannan ya yi kira ga iyaye da su matsa wajen kula da shige da ficen ‘ya’yan su.