An kama wani Lawal da ya boye wata ‘yar shekara 12 a gidan sa yana lalata da ita

0

Kotun sauraron karan dake Kubwa ta yanke wa wani mazaunin kauyen Byazhin a Kubwa mai suna Lawal Abubakar mai shekara 27 hukuncin ci gaba da zama a kurkukun ‘yan sanda saboda kama shi da laifin sata da yin lalata da ‘yar shekara 12.

Lauyan da ya shigar da karan Babajide Olanipekun ya fada a kotun cewa wani Abah Timothy mazaunin Byazhin a Kubwa ya kai kara a ofishin ‘yan sanda ranar 12 ga watan Disamba cewa Abubakar ya sace yarinyar bayan ya lallabata ya kai ta gidan sa a boye inda har tayi kwanaki uku ba a sani ba.

” Abah ya ce Abubakar ya yi ta lalata da yarinyar a tsawon zaman da tayi a gidan sa.”

Shi ko gogan naka Abubakar cewa yayi wai yarinyar budurwar sa ce ba sato ta ya yi ba.

Ya ce shigowa ta yi cikin gidan sa ta fada masa cewa iyayen ta basa nan sun yi tafiya wanda hakan ya sa ya barta ta kwana a gidan sa.

” Da garin Allah ya waye kuwa sai na duba gidan iyayen naga ko sun dawo, da naga basu dawo ba sai na bar ta ta ci gaba da kwanan ta abinta.”

Abubakar ya amince da cewa ya kwana da yarinyar a lokacin da take zama a gidan sa.

Daga karshe lauyan dake kare Abubakar ya roki alfarmar kotu da tayi wa Abubakar sassauci ganin ba laifin sa bane duk da na iyayen da suka yi tafiya suka bar yarinyar ita kadai a gida.

Share.

game da Author