An kama barauniyar yara a Masallaci

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai suna Juliet Ajagun a kotun sauron kara dake Ikeja da ta laifin sace wani yaro a masallaci.

Ita dai Juliet mai shekaru 38 na zama ne a layin Abuke, Ijegun sannan ana zargin ta da laifin sata da kuma hana mutane yin ibadar su cikin kwanciyar hankali.

Dan sandar da ya shigar da karar Clifford Ogu ya ce Juliet ta sace yaron ne a masallacin dake layin Muyi Opaleye, Ikeja ranar 12 ga watan Disamba a daidai mahaifiyar sa na sallah.

” Mun kama Julet ne da wannan yaron kafin ta fice daga masallacin bayan kwala ihu da wata mata tayi a cikin masallacin.”

Alkalin kotun Taiwo Akanni ya bada belin ta kan Naira 100,000 tare da shaidu biyu sannan ya daga sauraron karan zuwa 31 ga watan Janairu.

Share.

game da Author