An bautar da ‘yan Najeriya sama da 25,000 cikin 2017 a Libya – NAPTIP

0

Babban Daraktan Hukumar Hana Safarar Jama’a, NAPTIP, Julie Okah-Donli, ta bayyana cewa an bautar da ’yan Najeirya sama da 25,000 a Libaya, inda wasu kuma aka maida su karuwan karfi da yaji, ana lalata da su ba da son ran su ba.

Okah-Donli, ta yi wannan bayani ne a lokacin da ta ke kare kasafin kudin hukumar ta na 2018 a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa, a ranar Talata.

Ta kara da cewa a cikin shekarar nan, ta 2017, an dawo da kimanin 5000 zuwa Nijeriya. Yayin da ta kara da cewa an kuma dawo da wasu masu dimbin yawa daga Turai da wasu kasashe na Afrika.

Ta na mai karawa da cewa dukkan wadannan mutane da ake dawowa da su duk su na da bukatar tallafi, agaji tare da tantance yawan su.

Sai dai kuma ta nuna damuwar ganin yadda bautar da al’umma ke ta kara muni, amma kamar ba a cika maida hankali sosai kan batun ba.

Ta ce ayyukan da ke gabn hukumar ta masu dimbin yawa da wahala ne, amma kuma kasafin kudin hukumar bai taka kara ya karya, idan aka yi la’akari da dimbin aikin da ke gaban su.

Share.

game da Author