Allah yayi wa tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Gidado Idris rasuwa.
Gidado Idris dai shine Sakataren gwamnatin tarayya a mulkin marigayi Sani Abacha.
Abdulrahman Sambo, da ya tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar marigayi Gidado Idris ya ce za ayi jana’izan marigayi Gidado da karfe daya na ranar Asabar a Abuja.
Gidado Idris ya rasu ranar Juma’at a Abuja.