Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na da adadin ’yan Najeriya har 2,778 wadanda ke tsare a sansanoni daban-daban a kasar Libya, da ake ta kokarin dawo da su Najeirya.
Ma’aikatar Harkokin waje ce ta bayyana haka, a cikin wata takarda da jamai’in yada labaran ma’aikatar, Elias Fatile ya sanya wa hannu a ranar Talata, ya kara da cewa jami’an ofishin jakadancin Nijeriya da ke Libya su na ta bi sansanoni da dama domin tantance yawan ’yan Nijeriya da ke tsare.
Ma’aikatar ta ce dukkan wadanda aka kidaya sunan su, an ta ba su takardar iznin tafiya ko shiga Najeriya ta gaggawa.
Sanarwar ta kuma kara da cewa ta na aikin hadin kai da kungiyar kula da masu gudun hijira inda a duk sati ana dauko ‘yan Najeriya 250 daga Libya ana dawowa gida. Ya zuwa yau ta ce an dawo da ’yan Najeriya 3000 gida.