Dan majalisar Wakilai da ke wakiltar Bebeji/Kiru a majalisar Wakilai Abdulmumini Jibrin ya bayyana cewa ya ziyar ci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a matsayin sa na uba da da’.
Buhari da Jibrin sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa.
Koda yake bai bayyana abubuwan da suka tattauna ba wa manema Labarai, Jibrin ya ce ya ga Buhari cikin koshin Lafiya da annashuwa.
Yace bai San dalilin da ya sa karar sa kan da dakatar dashi ya makale a Kotu ba.
Majalisar Wakilai ta dakatar da Abdulmumini Jibrin a dalilin tona asirin coge da shugabannin majalisar ke yi a kasafin kudin kasa.
Daga karshe ya ce yayi amfani da ziyar da yayi fadar shugaban Kasa don yi wa dan sa Yusuf addua’ar samun Lafiya daga hadarin babur da yayi ranar Talata.