Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su samar da yanayin da za a rika zuba jari, a garuwuwa da manyan birane ana hada-hadar da za ta sammar wa matasa aikin yi.
A cikin wani jawabi da ofishin yada labaran Atiku ya yi wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja, Atiku ya ce kirkiro ayyukan yi ga bimbin matasan da ke watangaririya kan titi a kauyuka da cikin birane.
Ya ce yin haka zai rage hijirar da dubban matasa ke yi zuwa Libya da sauran kasashen da ake kashe su ko tozarta su.
Atiku ya yi jawabin ne domin tunatarwa ganin cewa yau Litinin ce ranar tunawa da ranar yin tir da kangin bauta a duniya.
Akwai dubban ‘yan Najeriya da ke jibge a Libya, masu son dawowa Najeriya saboda halin da suka tsinci kan su can.
Ya ce duk wanda aka ga ya bar gidan sa ya tafi wani gari nema, to can ta dara nan kenan. Ya na mai nuna takaicin cewa irin yadda matasa milyan uku suka rasa ayyukan su a cikin wannan shekara da kuma wasu mulyan uku a sekarar a ta wuce, to abin damuwa ne sosai.