Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke haramar kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Kano, kakakin yada labaran sa, Garba Shehu ya bayyana alheran da Kanawa suka samu a karkashin mulkin APC daga 2015 zuwa yau.
Shehu ya ce Buhari ya kawo zaman lafiya a Kano fiye da lokacin da gwamnatin da ta gabata ta bar Kano a ciki.
A jihar Kano ne dai Buhari ya fi samun yawan kuri’u har sama da miliyan 1.9.
A cikin wani rubutu da Shehu ya watsa a yau Litinin ya ce a baya “wasu batagarin ‘yan ta’adda ne suka addabi Kano da kashe-kashe da jefa bama-bamai a Kano, kamar yadda suka rika yi a wasu birane.
Yaa ce amma a yanzu zaman lafiya ya samu a Kano ko guje-guje an daina yi a Kano.
“Amma kafin hawan gwamnatin Buhari, babu inda ba ya fuskantar tashin hankali na babamai da muggan hare-hare. Jama’ar gari da jami’an tsaro duk sun dandana kudar su a lokacin.
“An ga bala’i daban-daban a Kano. Sai uwa ko uba su fita neman abincin da yaran su za su ci, amma kafin a jima sai a koma musu da gawarwagin su.
Shehu ya kara jaddada cewa a yanzu zaman lafiya ya dawo a Kano. An daina zaman dardar a ko’ina.
Garba Shehu ya ci gaba da cewa shugaba Buhari na ci gaba da dora jihar Kano a bisa turbar sauyin tattalin arziki ta hanyar kirkiro ayyukan ci gaba a jihar.
“A da an san Kano na a sahun gaba wajen kasuwanci, amma kafin hawan gwamnatin Buhari sai al’amarin ya ja baya, musammam dalilin matsalar ruwa.
“A da akan shafe kwanaki ba a samu hasken lantarki ba, hakan ya sa masana’antu suka durkushe, aka kori dubban ma’aikata daga aiki a masana’antu saboda idan an yi amfani da janareto a wasu masana’antun, to babu riba.
“Amma a yanzu abubuwa sai farfadowa suke kara yi. An fuskanci ayyuka da dama wadanda za su kara samar da lantarki, domin a yanzu a Kano ana samun lantarki a kowace rana, akalla awa 18.” Inji Garba Shehu.
Ya ce Kano za ta amfana da aikin jawo bututun gas daga Ajaokuta ya bi ta Abuja da Kaduna ya dire Kano.
“Wannan zai warkar da matsalolin da farfado masana’antu ke fuska sosai.
Sai ya lissafa wasu ayyukan titina da ake kan gudanarwa da suka hada da maida titin Kano zuwa Maiduguri mai falan biyu, da shi da kuma na Kano zuwa Potiskum da Damaturu, sai na Kano zuwa Katsina da kuma gyaran titin Saminaka zuwa Doguwa da tuka rititin Doguwa zuwa Tiga.
Ya kara da cewa titin Abuja zuwa Kaduna har Kano wanda aka sha korafi dangane da gyaran sa, an zu an sa himma ana kan aikin.
Ana aikin fadada filin saukar jirage na Kano da gyaran wuraren ajiye motoci a filin jirgin.
Sai kuma aikin titin jirgin kasa da Shehu ya ce Shugaba Buhari ya sa wa hannu daga Kano zuwa Maiduguri.
Ga kuma aikin titin jirgin na kasa har ila yau daga Lagos zuwa Kano, wanda shi hadin guiwa ne tsakanin Nijeriya da Chaina.
Akwai kuma aikin sake tantance masu amfana da tallafin N-Power, wanda Shehu ya ce saboda yawan matasa marasa aikin yi a Kano, gwamnati ta yanke shawarar a shigo da masu karatun shaidar NCE da Difiloma a ciki. Ya ce jihar Kano sama da matasa 80,000 ne suka cika fam na N-Power da ake kan tantancewa a hanlin yanzu.
Ya yi maganar ciyar da daliban firamare da ya ce cikin Disamba din nan zai kankama. Sai kuma tsarin agaji na CCT, wato cash transfer da ya ce an fara tun a ranar 23 Ga Nuwamba.
Discussion about this post