Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris, ya bada umarnin ‘yan sanda a fadin kasar nan su janye daga kafa shingen kan hanya su na tare motoci, wato “roadblocks.”
A maimakon haka, ya sake bada wani umarnin cewa a lokacin Kirismeti, jami’an nasa za su rika tsaida motoci su na binciken su, amma a wuraren da aka san sun yi kaurin-suna wajen tashe-tashen hankula da kuma mabuyar batagari.
Ya ce kuma jami’ar su rika gudanar da wannan bincike a cikin lalama da haba-haba da masu tuka ababen hawa. Ya na mai cewa kowane Kwamishinan ‘Yan Sanda a kowace jiha, ya tabbatar ya fito da kan sa domin ya ga yadda ake gudanar da wannan binciken, wanda sam shi ba shingayen-kan-hanya ne za a kafa ba.
Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su gaggauta kai rahoton duk inda suka ga wasu tsirarun ‘yan sanda sun kafa shingen duwatsu suna tare hanya da sunan “roadblocks” su na binciken motoci.
Kakakin Yadda Labaran rundunar ‘Yan sanda Moshood Jimoh, wanda ya bada wannan sanarwa, ya kuma ce Sufeto Janar Idris ya na taya al’umma murnar Kirsimeti, tare da fatan za a yi kuma a kammala bukukuwan lafiya.
Discussion about this post