Bayan fafatawa a karo na biyu da akayi tsakanin shahararren dan Kwallon kafan nan George Weah na Jam’iyyar CDC da mataimakin shugaban kasa mai ci Joseph Boakai na Jam’iyyar UP, Weah ya lashe zaben da kuri’u sama da 700,000.
Weah ya sami sama da kashi 60 bisa 100 na kuri’un da aka Kada inda Joseph ya sami kashi 38 bisa 100 na kuri’un da aka Kada a zaben.
George Weah ya gode wa mutanen Kasar sa sannan ya bayyana cewa kamar yadda jam’iyyar su na CDC ke da taken canji, jama’a suyi shirin ganin canji da sabon salon gudanar da mulkin a kasar.
” Zan maida hankali na, da karfi na wajen ganin mutanen Kasar mu sun shaida canjin da suka zaba.”
Discussion about this post