2019: INEC ta sa ranar zaben Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana ranar 16 Ga Fabrairu, 2019 a matsayin ranar da za a yi zaben Shugaban Kasa da kuma na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahood Yakubu ne ya bayyana haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a lokacin da ya ke jawabi wurin taron karin sanin makamar aiki da aka shirya wa Shugabannin Hukumar Zabe na Jihohi 36 har da Abuja.

Yakubu ya kara da cewa za a yi zabukan Gwamnoni, ‘Yan Majalisar Jihohi da Abuja a ranar 2 Ga Maris, 2019.

Shugaban na INEC ya kara bayyana cewa an kara yi wa mutane milyan 3,630,920 rajista, a wannan aikin rajista da aka soma kwanan nan.

GARGADI GA KWAMISHINONIN ZABE:
A gefe daya kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kakkausan gargadi ga kwamishinonin zaben kasar nan da su tashi tsaye ta hanyar hada karfi da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin a gano dukkan wuraren da ake hasashen cewa za a iya tayar da rikici a zaben 2019, domin a daukar masa mataki tun yanzu.

Yakubu ya kara da cewa duk da saura kwanaki 436 a kada kuri’a, INEC ba za ta kwanta, sai ranar tafiya sannan za ta fafe goran a ba. Ya ce a yanzu ne ya dace a magance komai, domin zaben ya tafi ba da wata tangarda ba.

“Wata babbar matsala ita ce yawaitar yada labaran kiyayya kan wani mutum ko rukunin jama’a da sunan. Siyisa. Wannan ma sai mun raba mun tashi mun gano masu yada wadannan labarai na kiyayya.

Daga nan ya ci gaba da cewa tun daga ranar 1 Ga Janairu, 2018 za a fara shirye-shiryen zaben 2019, domin a tari duk wani kalubalen da aka iya tasowa a lokacin zabe.

Share.

game da Author