2019: INEC ta kara bude cibiyoyin sabunta rajista 360 a kasar nan

2

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kirkiro Karin wasu cibiyoyin sabunta rajista (CVR) guda 10 a kokwace jiha har da Abuja. Hakan ya kai ga yawan cibiyoyin sabunta rajistar sun kai 672, tun daga lokacin da aka fara aikin sabuntawar cikin watan Afrilu na wannan shekarar.

Hukumar ta kuma kara da cewa ta yanke shawarar kara yawan cibiyoyin yin rajaistar ne domin a bai wa kowane dan Najeriya damar samun sabunta rajista ko yin wata, kafin zuwan zaben 2019.

Hukumar zabe dai ta fara wannan shirin yin rajista ne tun a ranar 27 Ga Afrilu, kamar yadda dokar zabe ta kasa ta 2010 ta bada iznin a yi.

Idan ba a manta ba, Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Mahmud Yakubu, ya sha jaddada cewa zaben 2019 zai fi dukkan sauran zabuka da aka yi a kasar nan inganci.

Share.

game da Author