2019: Har yau INEC ba ta sa ranar zaben-fidda-gwani ba

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta jaddada cewa har yau ba ta sa ranar da jam’iyyun siyasa za su yi zaben fidda gwanayen da za su tsaya musu takara a kukaman siyasa daban-daban a zaben 2019.

INEC ta fitar da wannan sanarwa ce ta hannun Daraktan Yada Labarai da Ilmantarwa kan Yin Rajista, Oluwale Osaze-Uzzi a ranar Litinin a Abuja.

A Osaze-Uzzi ya kara da cewa, wannan bayani ya zama tilas ganin yadda wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta bayyana cewa wai INEC ta sa ranar da za a yi zaben-fidda-gwani, kuma har wasu gidajen jaridu su ka dauki wannan baudadden labari su ka buga ba tare da tantancewa ba.

“Wannan ba gaskiya ba ne, kuma ba daidai ba ne. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ba ta aza wata ranar da jam’iyyun siyasa za su yi zaben fidda gwanin su a mukaman siyasa na zaben 2019 ba.

Ya ce kai ko jadawalin yadda zaben zai gudana ma INEC ba ta fitar ba. Domin jadawalin shi ne zai nuna ranakun da za a gudanar da komai dangane da shirye-shiryen zaben 2019.

” Amma nan ba da dadewa ba za a fitar da jadawalin domin kowa ya gani tun da wuri. Kuma duk za mu sanar wa jama’a baki daya ta hanyoyin da suka cancanta.”

Daga nan sai Osaze-Uzzi ya shawarci jam’iyyun siyasa, mambobin su da kuma jama’a baki daya da su yi watsi da labarin da su ka karanta cewa an sanar da ranar zabukan fidda gwanin.

Share.

game da Author