2019: Dalilin da ya sa Ibo za su zuba wa Buhari ruwan kuri’u -Uzor Kalu

0

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Uzor Kalu, ya bayyana cewa kabilar Ibo za su zuba wa Shugaba Buhari kuri’u a zaben 2919 domin kada su dagula tsarin fitar da shugaban kasa daga shiyya-shiyya.

Da ya ke magana a wata tattaunawa da ya yi da gidan Talbijin na Arise ranar Asabar da ta gabata, Kalu ya ce duk Ibon da bai zabi Buhari a 2019 ba, ya yi saki-na-dafe.

Ya na mai cewa, “2023 ita ce damar da ta fi kusa ga kabilar Igbo.”

A nan Kalu na nufin idan Buhari ya kammala zango na biyu a 2023, to dan kabilar Ibo ne zai zama shugaban kasa.

Batun karba-karba a tsarin shugabancin kasar nan dai an tsara cewa idan dan kudu ya yi mulki shekara 8, dan Arewa shi ma zai hau ya shekara takwas.

Sai dai an karya wannan sharadi a 2011, lokacin da Goodluck Jonathan ya fito takara bayan rasuwar Umaru Yar’Adua a 2010.

“Bayan Buhari ya kammala zango na biyu a 2023, ba wanda ya isa a Nijeriya ya fito ya fada mana cewa kabilar Igbo ba zai yi shugabanci a kasar nan ba.

” Ibo ba su goyi bayan sa a zaben 2015 ba, amma a 2019 za mu zuba masa kuri’a. Ina gaskata shi ne saboda ya na da dattako.

“Bankin Duniya kansa da Kungiyar Tarayyar Turai sun yarda da Buhari da ma sauran manyan shugabannin kasashen duniya.” Inji Kalu.

A karshe ya ce, “Idan Buhari ya ci zabe a 2019, to nasarar Buhari nasarar kabilar Ibo ce.”

Share.

game da Author