ZAZZABI: A Kaduna mun fi amfani da maganin gargajiya

0

KEBBI

Gwamnatin jihar Kebbi ta Koka kan yadda zazzabin cizon sauro a jihar ya addabi mutane duk da cewa ta na kokarin ganin an sami raguwa da kamuwa da cutar.

Wani mai sana’ar siyar da magani a Birnin Kebbi ya ce sama da kashi 60 bisa 100 na magugunan da suke siyarwa maganin cutar zazzabin cizon sauro ne.

Mazauna jihar sun ce “abin na ci musu tuwa a kwarya musamman yadda suke shan magani cutar amma ba su samin sauki.”

Duk da haka ma’aikatar kiwon lafiya na jihar ta ce gwamanti ta ware kudade da dama wajen yi feshin hanyoyin ruwa da wasu dazuka dake jihar.

Ya ce gwamantin ta horar da ma’aikata na musamman wandanda za su dunga yin feshi duk bayan wata 6.

KANO

A jihar Kano mutane sun koka kan yadda suke yawan fama da cutar zazzabin cizon sauro a jihar.

Wani mai sana’ar siyar da magunguna a karamar hukumar Nasarawa Yahuza Danbaba ya ce sun fi samun ciniki ne a sana’ar su tsakanin watannin Agusta da Oktoba.

Ya ce wannan lokacin mutane sun fi fama da zazzabin cizon sauro. Mutane sukan yawaita zuwa shagunan mu domin siyan magani. Mukan siyar wa mutane maganin ne daidai iya kudin kutum. Sannan yakan kama ne daga naira 800 zuwa 4500.

Wasu mazaunan jihar sun ce sanadiyyar rashin tsaftace muhalli da amfani da gidanje sauro ne yasa ake yawan kamuwa da cutar a jihar.

Ma’aikaciyar asibitin Aminu Kano Halima Adamu ta ce rashin shan magungunan cutar daidai yadda aka ce asha na dawo da cutar.

Ta kuma kara da cewa dalilin da ya sa akan yi fama da cutar a watanin Agusta zuwa Oktoba shine don lokacin damina ne sannan da rashin kyawawan hanyoyin ruwa da jihar ke fama da su.

” Barin ruwa a cikin tukunya da sauran wurare ne ke haifar da sauro su kuma buwayi mutane.”

Ya ce maganin ‘Chloroquine’ baya warkar da cutar zazzbin cizon sauro. Ya ce maganin da ya kamata a yi amfani da shi shine ‘Artemisinin- based combination therapies (ACTs).

KADUNA

Mazaunan jihar Kaduna kuwa sun gwammace su yi amfani da magungunan gargajiyya don kawar da cutar zazzabin cizon sauro da su yi amfani da na asibiti.

Mutanen Kaduna sun ce saboda rashin samun magani na kwarai ne ya sa mutane ke yin amfani da maganin gargajiya.

Wanimai suna Umar Faruk ya ce makonni biyu cur yayi yana fama da zazzabin cizon Sauro amma sauki ya gagara shine fa ya koma yin amfani da na gargajiya. ” Cikin Ikon Allah kuwa na sami lafiya

Wata ma’aikaciyar asibitin dake zaman kanta a Kakuri, Kaduna ta ce idan ka ga mutane 50 na jiran ganin likita a asibiti 40 daga cikin su, na fama da zazzabin cizon sauro ne.

SOKOTO

“An kashe Naira miliyan 250 wajen siyo magungunan sauron da zaa yi feshin da shi sannan da biyan ma’aikatan feshi 1,500 da aka dauka.” Jami’in kiwon lafiya ya ce.

Gwamanti ta raba magungunan cutar kauta wa yara kanana da suka kai yawan miliyan daya.

KATSINA

Kananan hukumomi 4 cikin 34 dake jihar sun yi fama da cutar maleriya a shekaran nan.

Kananan hukumomin da suka yi fama da wannan cutar sun hada da Baure,Dutsi,Mai’adua da Mashi.

Bayanan sun nuna cewa yara 2000 yan shekar 6 a jihar na samun alluran rigakafin cutar duk lokacin damina.

Share.

game da Author